EU ta baiwa WHO tallafin Euro miliyan 400 don samar da rigakafin korona

Maganin rigakafin cutar korona
Maganin rigakafin cutar korona REUTERS/Dado Ruvic/Illustration

Kungiyar Tarayar Turai ta sanar da shirin mika kudade da suka kai Kudin Turai Euro Miliyan 400 ga Hukumar Lafiya ta Duniya domin sayan magungunan cutar coronavirus da duniya keta hakilon neman maganin yanzu haka.

Talla

Karkashin shirin da Hukumar Gudanar Kungiyar Tarayar Turai ta gabatar za’a yi amfani da kudaden ne don sayo magungunan warkar da cutar korona miliyan biyu nan da karshen shekara ta 2021 don baiwa dukkan kasashen duniya.

A cewar wata jami'a a kungiyar kasashen za’a samo wadannan kudade ne karkashin wani tallafi da suka shata.

A cewar Shugaban Hukumar kungiyar kasashen na Turai Ursula Von Der Leyen matakin na biyo bayan bukatar dake akwai ne na agazawa mutane marasa karfi a sassan duniya.

Wannan ne yasa Hukumar tuntuban dukkan manyan kamfanonin harhada magunguna dake duniya don ganin an samo maganin wannan cuta, kuma cikin rahusa ga kowa da kowa.

Sai dai kuma duk da wannan , wasu masu adawa da matakin na ganin wannan dabara ce don ganin kokarin da Hukumar Lafiya ke yi bai yi wani tasiri ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI