Birtaniya

Birtaniya ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da Japan bayan samun baraka da EU

Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson. Andrew Parsons/No 10 Downing Street/Handout via REUTERS

Birtaniya ta kammala kulla yarjejeniyar kasuwanci irinta ta farko da Japan wadda darajarta ta haura fam biliyan 15 kwana guda bayan samun farraka da tarayyar Turai kan matakin sauya yarjejeniyar rabuwarsu.

Talla

Sashen kasuwanci na Birtaniya da ke sanar da matakin kulla yarjejeniyar kasuwancin don taimakar tattalin arzikin juna a yau Juma’a, ya ce yarjejeniyar za ta maye gurbin makamanciyarta da ke tsakanin Japan da EU a baya.

An dai yi nasarar kulla yarjejeniyar tsakanin kassahen na Japan da Birtaniyar ne ta bidiyon Intanet bisa halartar sakataren kasuwancin Japan Toshimitsu Motegu da sakataren kasuwanci na kungiyar kasuwanci ta duniya Liz Truss baya ga mahukuntan Birtaniya.

Tun cikin watan Janairun da ya gabata ne Birtaniya ta kammala ficewa daga kungiyar shekara 4 bayan kada kuri’ar raba gardamar ficewar kasar, sai dai ta na da wa’adin daga wancan lokaci zuwa har karshen shekarar nan don kammala kulla yarjejeniyar kasuwanci tsakaninta da kasashen EU.

Sai dai a jiya Alhamis baraka ta sake fitowa karara tsakanin Birtaniyar da EU bayan da Brussels ta yi watsi da bukatar aiwatar da sauye-sauye kan yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kammala kullawa.

Sashen kasuwancin na Birtaniya ya bayyana cewa yarjejeniyar kasuwancin tsakaninsu da Japan manuniya ce ga EU kan yiwuwar kasar ta karkata akalar kasuwancinta zuwa wasu sassa ba lallai nahiyar ta Turai ba.

A ranar 1 ga watan Janirun mai zuwa ne yarjejeniyar Birtaniyar da Japan za ta fara aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.