Faransa

Faransa: Sama da mutane dubu 10 sun kamu da coronavirus a rana 1

Wasu ma'aikatan lafiya a Faransa, yayin kula da wani mai cutar coronavirus
Wasu ma'aikatan lafiya a Faransa, yayin kula da wani mai cutar coronavirus © Joel Saget / AFP

Ma’aikatar lafiyar Faransa tace a karon farko tun bayan bullar annobar coronavirus cikin kasar, mutane dubu 10 da 561 sun kamu da cutar a rana guda.

Talla

Sabbin alkaluman sun zo ne, jim kadan bayanda a ranar Juma’a Fira Ministan Faransa Jean Castex yayi gargadin cewa ba shakkah sake barkewar annobar ta coronavirus na cigaba da yin muni a sassan kasar.

Sai dai Firaministan yace ba za su sake killace daukacin al’ummar kasar kamar yadda aka yi a zangon farko ba, inda a maimakon hakan za su yaki annobar ta hanyoyin hana cinkoson jama’a, sanya takunkumin rufe naki da hanci, kara saurin yiwa mutane gwaji da kuma takaita sa’o’i da kasuwanni za su kasance a bude.

A ranar Alhamis ta makon jiya ce Faransar ta kafa tarihin samun mutane kusan dubu 10, bayanda da jami’an lafiya a kasar suka tabbatar cewa mutane dubu 9 da 842 da suka kamu da coronavirus a rana guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.