Girka-Turkiya

Girka za ta yiwa rundunar sojinta garambawul irinsa na farko cikin shekaru 20

Jirgin yaki kirar Rafale da Girka za ta sayi 18 daga Faransa
Jirgin yaki kirar Rafale da Girka za ta sayi 18 daga Faransa Prakash SINGH / AFP/File

Fira Ministan Girka Kyriakos Mitsotakis yace gwamnatinsa za ta sayi makamai masu yawan gaske gami da yiwa rundunar sojin kasar garambawul, a daida lokacin da zaman tankiya ke karuwa tsakanin kasar ta Girka da Turkiya a gabashin Meditaraniya.

Talla

A karkashin shirin karfafa rundunar sojin nata mafi girma da aka gani a kusan shekaru 20, Girka ta cimma matakin sayen jiragen yaki 18 daga Faransa kirar Rafale, da jiragen yaki masu saukar ungulu na zamani guda 4, sai kuma daukar sabbin sojoji dubu 15, bayaga kara yawan makudan kudade a kasafin da take baiwa rundunar sojin nata, a bangaren kere-kere da kuma fasahar sadarwa.

Wani lokaci a yau lahadi ake sa ran Fira Ministan Girka zai yi karin bayani kan wannan shiri, da ya cimma aiwatarwa bayan ganawarsa da shugaban Faransa Emmanuel Macron, kan takaddamar da ta kunno kai tsakaninsu da Turkiya kan arzikin mai da iskar gas dake iyakokinsa a gabashin tekun Meditaraniya.

A bangaren Turkiya kuwa, a karshen makon nan shugaba Recep Tayyib Erdogan ya gargadi Faransa da cewar za ta dandana kudarta, muddin ta cigaba da yin katsalandan a rikicin arzikin kan iyakar dake tsakaninta da kasashen Girka da kuma Cyprus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.