Faransa

Masu rigunan dorawa sun cigaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa

Masu sanye da rigunan dorawa yayin zanga-zanga a tsakiyar birnin Paris
Masu sanye da rigunan dorawa yayin zanga-zanga a tsakiyar birnin Paris AFP

Bayan daukar lokaci ba tare da jin duriyarsu ba sakamkon annobar coronavirus da ta takaita zirga-zirga gami da taruwar jama’a, masu sanye da rigunan dorawa dake adawa da gwamnatin shugaban Faransa Emmanuel Macron, sun cigaba da zanga-zanga a ranar Asabar, abinda ya kai ga arrangama tsakaninsu da ‘yan sanda a birnin Paris, Lyon da kuma Tolouse.

Talla

Sai dai a wasu biranen zanga-zangar ta gudana cikin lumana, zalika burin masu jagorantarta bai cika ba na fatan fitowar dubban jama’a, domin kwatanta irin dimbin magoya bayan da suke da a watannin baya.

Ministan cikin gidan Faransa Gerard Darmanin yace jumillar mutane kimanin dubu 8 da 500 ne suka fita zanga-zangar masu rigunan dorawar dake adawa dasu, daga cikinsu dubu 2 da 500 a birnin Paris.

A watan Nuwamban shekarar 2018 lokacin da zanga-zangar masu rigunan dorawar ke kan karfinta a Faransa ne aka taba samun makon da akalla mutane dubu 300 suka fita zanga-zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.