Belarus

An cafke daruruwan 'yan adawar Belarus

Jami'an 'yan sandan Belarus sun cafke daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnati.
Jami'an 'yan sandan Belarus sun cafke daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnati. Sergei GAPON / AFP

Jami’an tsaro sun cafke magoya bayan ‘yan adawa akalla 250 a zanga-zangar nuna hamayya da Alexander Lukashenko a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugabancin kasar Belarus cikin watan jiya.

Talla

Mako na hudu a jere, a jiya lahadi ma sama da mutane dubu 100 ne suka fantsama kan titunan birnin Minsk fadar gwamnatin kasar ta Belarus, inda suka bukaci shugaba Alexander Loukashenko ya sauka daga kagarar mulki.

To sai dai kamar yadda aka saba, ko a wannan karo jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da motocin ruwan zafi domin hana tarzomar, yayin da majiyoyi daga ‘yan adawar ke cewa an kama mutane akalla 400 a jiya Lahadi kawai.

Jagorar ‘yan adawar wadda ke gudun hijira a makociyar kasar wato Lutiania Svetlana Tikhanovskaya, ta bukaci magoya bayanta su ci gaba da jajircewa har sai  shugaba Loukashenko ya yi marabus.

Loukashenko, wanda ya dare kan karagar mulkin kasar ta Belarus tun 1994, na zargin kasashen Yamma da mara wa ‘yan adawar baya, yayin da shi kuma yake samun goyon bayan shugaba Vladimir Putin na Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.