Birtaniya-EU

Kimar Birtaniya na fuskantar barazanar zubewa-EU

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson REUTERS/Toby Melville/Pool

Tarayyar Turai ta ce kimar Birtaniya na fuskantar barazanar zubewa a daidai lokacin da bagarorin biyu ke kokarin warware dangantakar kasuwanci da ke tsakaninsu tsawon shakaru 50 biyo bayan wata kuri’ar jin ra’ayi da ta raba kan al’ummar kasar.

Talla

Tarayyar Turai ta yi watsi da ikirarin da firamistan Birtaniya Boris Johnson ya yi cewa tana kitsa manakisar wargaza kasarsa, a yayin da aka shiga wani makon da za a ci gaba da tattaunawa mai sarkakiya don cimma yarjejeniya kan yadda kasuwanci zai kasance bayan rabuwa.

Yakin cacar baki tsakanin bangarorin biyu ya kazanta ne sakamakon wani sabon kudirin da Johnson ya gabatar, wanda Birtaniyar da kanta ta ce lallai ya saba wa tanade-tanaden yarjejeniyar yin hannun riga ta Turai, lamarin da ya janyo martani cikin fushi daga tsaffin firamistocin kasar Tony Blair da John Major, da ma ‘yan majalisar dokokin kasar.

Major da Blair wadanda su suka jagoranci tattaunawar zaman lafiyar yankin Ireland mai dimbim tarihi a cikin shekarun 1990’s, a jiya Lahadi sun ce matakin gwamantin Birtaniya abin kunya ne ga kasar.

Johnson ya yi zargin cewa kungiyar Tarayyar Turai na shirya manakisar kawo tarnaki wajen shigowar kayan abinci kasar, ta wajen jerin shamaki da ta bijiro da su a harkar kasuwanci tsakanin Birtaniya da arewacin Ireland, zargin da Ministan Harkokinn Wajen Ireland, Simon Coveney ya ce babu gaskiya a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.