Belarus

Lukashenko zai iya warware rikicin siyasar Belarus - Putin

Vladmir Putin  Shugaban kasar Rasha
Vladmir Putin Shugaban kasar Rasha Kirill KUDRYAVTSEV / AFP

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce cewa takwaransa na kasar bélarusse Alexandre Lukachenko zai iya warware rikicin siyasar dake faruwa a kasarsa, sakamakon  jerin zanga zangar da ake ci gaba da yi tun bayan sake zabensa kan karagar shugabancin kasar a watan ogustan jiya.

Talla

A lokacin da yake tsokaci kan gyaran fuskar da Alexendre Lokachenko ya yi alkawalin yi wa kundin tsarin mulkin kasar ta Belarus a matsayin wata mafita ga rikicin siyasar dake ci gaba da tashi a kasar,shugaban Rasha Vladimir Poutine ya ce ya gamsu da kwarewar da shugaba Lukashanko ke da ita ta fannin siyasa, wanda zai baiwa kasar ta Bélarus damar cimma sabin iyakoki, kamar yadda hoton vidion ganawar da ta shiga tsakanin shuwagabanin 2 a Sotchi (sud) da tashar da tashar talabijin din kasar ta Rasha ta yada ya nunar.

Lukachenko dai na ci gaba da fuskantar zanga zangar yan adawa da kungiyoyin fararen hula dake samun goyon bayan kasashen turai ne, tun bayan da hukumar zaben kasar ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da kimanin kashi 80%

Al’ummar Belarus dai na kwadayin samun sauyin shugabanci ne, bayan da shugaba Alexendre Loukachenko dake kawancen kunt da kut da kasar Rasha ya share sama da shekaru 25 yana mulkin kasar Belarus dake yankin gabashin nahiyar turai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.