Faransa

Macron ya bukaci Putin ya yi karin haske a kan yunkurin kisan jagoran 'yan adawa

Le président Emmanuel Macron, lors d'une conférence de presse à Ajaccio, en Corse, le 10 septembre 2020.
Le président Emmanuel Macron, lors d'une conférence de presse à Ajaccio, en Corse, le 10 septembre 2020. Ludovic Marin/Pool via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci bayni daga takwaransa na Rasha Vladimir Putin dangane da yunkurin kisan jagoran ‘yan adawan kasarsa Alexei Navalny, amma Putin ya mayar da martani yana mai cewa zargin shayar da Navalny guba ba shi da tushe ballantana makama.

Talla

Bayan gwaje gwaje a Faransa da Jamus sun tabbatar da cewa guba samfurin Novichok, mai katse hanyoyin jini aka shayar da Navalny, Shugaba Macron ya shaida wa Putin cewa yana da mahimmanci ya yi karin haske ba tare da bata lokaci ba a game da lamarin da ya kusan aike da jagoran ‘yan adawan barzahun.

Macron ya ce nazarin da Faransa ta yi ya tabbtar da zargin Jamus na cewa gubar Novichok aka dura wa Navalny, abin da ya yi karan tsaye ga dokokin kasa da kasa na amfani da makamai masu guba.

Wannan guba ce aka yi amfani da ita wajen kai wa tsohon jami’in leken asirin Rasha Serge Skripal hari a shekarar a 2018.

A can Moscow, Putin ya yi watsi da zargin da ake wa gwamnatinsa na amfani shayar da Navalny guba mai matukar hatsari a matsayin mara tushi ballantana makama.

Macron dai na ta kokarin inganta manufar samun kusanta da Rasha, inda yake neman ci gaba a bangaren kawo karshen rikicin Rasha da Ukraine, matakin da abokansa na Turai ke diga ayar tambaya a kai.

Amma masu fashin baki na cewa shayar da Navalny guba, da ya kai har yanzu yana kwance a gadon asibiti a Jamus ya yi wa dangantaka tsakanin Faransa da Rasha kwarzane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.