Rasha

An bukaci Turai ta sanya wa Rasha takunkumi saboda Novichok

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin Alexei Druzhinin / SPUTNIK / AFP

Majalisar Dokokin Kasashen Turai ta bukaci shugabannin yankin da su kakaba wa Rasha takunkumi kan abin da ta kira amfani da sinadari mai guba da aka dirka wa shugaban 'yan adawar kasar Alexei Navalny da zummar hallaka shi.

Talla

'Yan majalisun sun ce amfani da sinadarin Novichok wajen kai hari kan Navalny wani yunkuri ne na murkushe 'yan adawa da gwamnatin shugaba Vladimir Putin ke yi.

Majalisar ta ce kashe 'yan siyasa da kuma sanya musu guba ya zama wata hanyar da gwamnatin Rasha ke amfani da ita wajen rufe bakin 'yan adawa, ganin yadda sojoji ne kawai ke da alhakin mallakar sinadarin na Novichok.

Majalisar ta bukaci kungiyar Turai da ta gaggauta tsara matakan karfafa matsin lamba kan gwamnatin Rasha wajen dora wa kasar karin takunkumi, duk da yake Majalisar ba ta da hurumin daukar matakin a dokance.

Kungiyar Kasashen Turai ta sanya wa Rasha takunkumi bayan da aka yi amfani da sinadari mai guba wajen kai hari kan Sergei Skripal, wani tsohon jami’in leken asirin kasar da ‘yarsa a London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.