Belarus

Belarus ta gargadi EU kan gayyatar Tsikhanouskaya taron ministocin Turai

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko.
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko. REUTERS/Vasily Fedosenko

Gwamnatin Belarus ta gargadi kungiyar Tarayyar Turai kan hadarin da ke tattare da gayyatar jagorar adawar kasar Sviatlana Tsikhanouskaya zuwa taron ministocin kungiyar da zai gudana, yunkurin da Belarus ta bayyana a matsayin kokarin yi mata katsalandan a harkokinta na cikin gida.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Belarus da ke aikewa EU gargadin ta ce gayyatar ‘yar adawar taron na makon gobe tamkar rura wutar rikicin siyasar da kasar ke fuskanta ne a yanzu haka.

Tsikhanouskaya dai na kokarin kawo karshen mulkin shugaba Alexander Lukashenko da ya shafe shekaru 26 yana mulkar kasar.

Tun farko kafofin yada labaran Rasha ne suka sanar da cewa, EU na kokarin gayyatar ‘yar adawa Tsikhanouskaya zuwa taron a wani yunkurin nuna mata cikakken goyon baya kan gwagwar,ayarta duk da cewa ta na ci gaba da gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.