Sama da mutane dubu 13 sun kamu da cutar coronavirus a rana 1
Wallafawa ranar:
Gwamnatin yankin Nice a Faransa ta haramta taron sama da mutane 10, gami da takaita sa’o’in bude wuraren shan barasa, bayanda hukumomin lafiya a kasar suka bayyana samun adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a rana 1.
Sabbin alkaluman ma’aikatar lafiyar Faransa sun ce mutane dubu 13 da 215 ne suka kamu da cutar a jiya Juma’a kadai adadi mafi girma da kasar ta gani, tun bayan barkewar annobar cikinta.
A makon jiya ne dai al’ummar kasar ta Faransa suka soma ganin daya daga cikin adadi mutane mafi muni da suka kamu da cutar ta coronavirus a rana 1, inda akalla mutane dubu 10 da 593 suka harbu da cutar.
Sai dai duk da sake barkewar annobar dake yaduwa cikin sauri a sassan Faransa karo na 2, Fira Ministan kasar Jean Castex yace ba za a sake killace daukacin al’ummar kasar kamar yadda aka yi da fari ba, a maimakon hakan za a dauki matakin ne kan yankunan da cutar tafi muni, cikinsu har da biranen Lyon da Marseille.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu