Amurka

Shugabar alkalan kotun kolin Amurka ta mutu

Shugabar alkalan kotun kolin Amurka Ruth Bader Ginsburg.
Shugabar alkalan kotun kolin Amurka Ruth Bader Ginsburg. REUTERS/Lindsay DeDario

Babbar alkaliyar kotun kolin Amurka Ruth Bader Ginsburg daga ake wa lakabi da RBG ta mutu a jiya Juma’a ta na da shekaru 87, bayan fama da cutar Kansa.

Talla

Kafin rasuwarta Ginsburg ce Alkaliya mafi tsufa daga cikin alkalan kotun kolin Amurka guda 9.

Wasu dai na kallon mutuwar babbar Alkaliyar zai janyo gibin da zai kara zafafa adawar siyasa a Amurkan tsakanin jam’iyyar Repulican da Democrats, a daidai lokacin da zaben shugabancin kasar ke dada matsowa.

Yanzu haka dai kwanaki 45 suka ragewa zaben shugabancin Amurka, wanda kuma kafin gudanarsa ne shugaba Donald Trump da jam’iyyarsa ta Republican ke fatan maye gurbin Ruth Bader da alkalin da zai marawa manufofinsu baya, da suka hada da takaita ‘yancin zubar da ciki, karawa manyan ‘yan kasuwa karfi, da kuma dakile ‘yancin da aka baiwa masu ra’ayin auren jinsi guda a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.