Faransa

Adadin masu coronavirus na kara hauhawa a Faransa

Wasu Faransawa a birnin Paris, yayin jiran yi musu gwajin cutar coronavirus.
Wasu Faransawa a birnin Paris, yayin jiran yi musu gwajin cutar coronavirus. REUTERS/Charles Platiau

Adadin mutanen dake kamuwa da cutar coronavirus na cigaba da hauhawa a Faransa, inda a yanzu jumillarsu ya kai dubu 442, da 194, bayanda aka cika kwanaki 7 a jere, ana samun karin mutane sama da dubu 9 dake kamuwa da cutar a kowace rana, idan aka kwatanta da adadin 272 da aka samu a karshen watan Mayu.

Talla

Ma’aikatar lafiyar Faransa tace a jiya asabar kadai, karin mutane dubu 13 da 498 aka gano dauke da cutar ta coronavirus, wanda kuma ko a Juma’ar da ta gabata kadai, karin masu dauke da cutar dubu 13 da 215 aka samu.

Ya zuwa wanna lokaci dai jumilar mutane dubu 31 da 274 annobar ta halaka a Faransa, bayan samun karin mutane 26 a jiya da cutar ta kashe.

A makon da ya kare hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana kaduwa kan karuwar adadin mutanen da annobar coronavirus ke halakawa a sassan duniya, wadda tace sabbin alkalumanta sun nuna cewar, kusan rayuka dubu 50 cutar ta lakume a mako 1.

Sake barkewar annobar ta coronavirus a sassan Turai, ya sanya hukumomin wasu kasashen nahiyar daukar matakan sake killace wasu daga cikin yankunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.