EU-Libya

EU ta sanya takunkumi kan kamfanoni 3 da suka shigar da makamai Libya

Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. AP/Olivier Hoslet/Pool

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da sanya takunkumai kan wasu kamfanoni 3 da suka karya dokar haramcin shigar da Makamai kasar Libya mai fama da rikici.

Talla

Kamfanonin 3 da suka kunshi guda a Turkiya wani daban a Kazakhstan kana wani a Jordan, wata majiyar Diflomasiyya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa tuni ministocin wajen kungiyar ta EU suka aminta da kakaba musu takunkuman da zai haramta musu shiga a dama dasu cikin harkokin cinikayyar kasashen kungiyar.

Takunkuman kan kamfanonin 3 su hada da kulle asusunsu da ke kasashen EU da kuma haramta musu hada hada da kassahen na EU kana dakatar da su a kasuwancin nahiyar Turai.

Yayin taron na EU a Brussels, ministocin sun kuma kakaba makamantan takunkukuman kan wasu dai daikun mutane 2 da kungiyar ta zarga da laifin shigar da makamai ga Khalifa Haftar wanda ke samun damar ci gaba da farmakar gwamnatin kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

EU wadda ta kafa sansanin Sojin Ruwa na musamman a gab da Libya da nufin dakile masu kokarin karya dokar haramcin shigar da makamai kasar, tun a wancan lokaci sai a yau litinin ne kungiyar ta taba sanar da makamancin takunkumin kan masu kokarin yiwa dokar karantsaye.

Kusan shekaru 10 kenan Libyan na fama da rikici, tun bayan yamutsin 2011 da ya kai ga hambarar da gwamnatin Moamer Kadhafi baya ga kisansa da sauran manyan mukarraban gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.