Faransa-MDD

Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar matsalolin da ke hana ruwa gudu-Macron

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Julien DE ROSA / POOL / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince da cewar Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar matsalolin da suka hana ruwa guda, inda ya bukaci hadin kai domin tinkarar matsalar.

Talla

Yayin da yake jawabi ga taron Majalisar na 75 ta kafar bidiyo, shugaba Emmanuel Macron yace tabbas ginshikin ginin Majalisar ya rawa, sakamakon tsagewar da wadanda suka kafa ta suka haifar, musamman ganin yadda Amurka ke kauracewa wasu daga cikin hukumomin Majalisar a cikin shekaru 3 da suka gabata.

Macron ya ce wasu batutuwa da a baya ake kallon su a matsayin haramtattu yau sun zama abin yi, kamar yadda kasashen da suka fi karfi kan mamaye marasa karfi da yadda ake amfani da makamai masu guba da tsare jama’a ba tare da sun aikata laifi ba.

Shugaban yace ‘yancin da ada ake ganin an samu yau sun gushe saboda yadda shugabanni ke take su, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta gaza wajen hukunta masu aikata irin wannan aika aika.

Macron yace yayin da annoba ke cigaba da yiwa duniya illa, matsaloli yanzu haka su shan kan kasashe, wadanda suka hada da na lafiya da sauyin yanayi da ‘yanci, inda ya zama wajibi duniya ta hada hada kai wajen shawo kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.