Faransa

Mataimakin Jam'iyyar shugaba Emmanuel Macron ya yi murabus

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Ludovic Marin/Pool via REUTERS

Mataimakin Jam'iyyar shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi murabus daga mukaminsa a wannan Litinin, yana mai bayyana matakin na sa a matsayin lamari mai bada firgici.

Talla

Jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron ta Republic on the Move wadda aka kafa ta a shekarar 2017 lokacin zaben shugaban kasa, na fuskantar masassara a daidai lokacin da Macron ke shirin neman sabon wa ‘adi a zaben 2022.

Mataimakin nasa, Pierre Person wanda ya yi murabus, zai ci gaba da zama mamba a jam’iyyar, yayin da ya shaida wa Jaridar Le Monde cewa, ya sauka daga kujerarsa ce domin bai wa jam’iyyarsa damar numfasawa.

A cewarsa, yana son haddasa kaduwa mai tayar da hankali a daidai lokacin da jam’iyyar ke ci gaba da kankame akidar da ta gabatar tun lokacin yakin zaben shugaban kasa na shekarar 2017.

Murabus din Person mai shekara 31, na zuwa ne bayan jam’iyyarsu ta samu jerin koma-baya a zabukan kananan hukommmi da aka gudanar a farkon wannan shekara.

Kazalika rahotanni sun ce, Person na takun saka da shugaban jam’iyyar ta Republic on the Move, wato Stanislas Guerini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI