Birtaniya-Coronavirus

Birtaniya ta fara daukar matakan killace jama'a a karo na 2 saboda Covid-19

Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson. Andrew Parsons/No 10 Downing Street/Handout via REUTERS

Gwamnatin Birtaniya ta tsaurara matakan kariya don dakile sake yaduwar annobar Coronavirus, ta hanyar umartar shagunan cin abinci da gidajen nanaye su rufe da wuri, abin da ke nuni da cewa ta yi watsi da kiraye kirayen da ta ke wa al’umma su dawo aiki da zummar ceto tattalin arzikin kasar da ya fita hayyacinsa.

Talla

Birtaniya na bin sahun nahiyar Turai wajen tinkarar bullar cutar coronavirus a karo na biyu, kuma Firaminista Boris Johnson na cewa akwai bukatar daukar matakai a yanzu don kauce wa daukar wadanda za su fi wannan tsauri da tsada.

Johnson ya ce matakan da za a dauka na iya shafe tsawon watanni 6, kuma za a tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda ya keta daya daga cikin ka’idoji da aka gindaya, yana mai cewa idan dukkannin matakan da suka dauka sun gaza cin karfi wannan cuta, ya zama wajibi su sake daukar wasu matakai masu tsauri.

Kwararru da ke aiki da gwamnati a wajen yaki da wannan cuta sun yi wani hasashe mai razanarwa, inda suke cewa idan har aka gaza daukar mataki, tabbaci hakika za a samu masu harbuwa da wannan cuta dubu 50, tare da mutane dubu 200 da cutar za ta kashe kowace rana.

Daga ranar Alhamis mai zuwa, za a fara rufe gidajen cin abinci da karfe 9 na dare agogon GMT, yayin da zai zame wa ma’aikatansu dole su sanyan mayanin kariya.

Daga Litinin, mutane 15 ne kawai za a bari su halarci walimar daurin aure, wajen jana’iza kuma mutane 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.