Belarus

EU ta gaza kakaba wa Belarus takunkumi

Shugaban Belarus, Alexandre Loukachenko
Shugaban Belarus, Alexandre Loukachenko BelTA via Reuters

Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Turai sun gaza cimma matsaya kan kakaba wa Belarus takunkumi  duk da magiyar da jagorar ‘yan adawar kasar, Svetlana Tikhanovskaya ta yi musu a kan hakan.

Talla

Belarus ta fuskanci irin zanga-zangar da ba ta taba gani ba a tarihinta, tun bayan da shugaban kasar Alexander Lukashenko ya yi ikirarin sake lashe zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar 9 ga watan Agusta, ya kuma yi dirar mikiya a kan masu zanga-zangar.

Tikhanovskaya ta gana da ministocin harkokin wajen kasashen Turan a birnin Brussels, inda ta bukaci su lafta wa Lukashenko takunkumi, amma duk da tulin sanarwai da suka caccaki irin ta’asar da shugaban ya yi tare da barazanar daukar matakai, babu abin da kungiyar ta yi.

Cyprus wacce ke da dangantakar kud da kud tsakaninta da Rasha, babbar mai goya wa Lukashenko baya ta ki yarda da batun kakaba wa shugaban na Belarus takunkumi, tana mai zakewar cewa dole a sanya wa Turkiyya takunkumi rikicin hakar gas a gabashin Tekun Mediterranean a lokaci daya.

Ministan harkokin wajen Cyprus Nikos Christodoulides ya kare matsayin kasarsa, inda yake cewa dole Tarayyar Turai ta dau mataki na bai daya a game da batutuwan da suka shafe take 'yancin cin gashin kai da hakkin bil adama.

Tarayyar Turai za ta gana a kan wannan batu a taronta na ranar Alhamis mai zuwa a birnin Brussels.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.