Majalisar Dinkin Duniya-Macron

Macron ya nemi kasashe su kau da kai daga cacar bakin Amurka da China

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Julien DE ROSA / POOL / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su kaucewa barin rikicin da ke gudana tsakanin China da Amurka su mamaye harkokin da ke gaban su, a daidai lokacin da ya ke bukatar samun sabon hadin kan da zai bayar da damar shawo kan matsalolin da suka addabi duniya.

Talla

Yayin da ya ke gabatar da jawabi a Majalisar Dinkin Duniya ta bidiyo, shugaban ya ce babu yadda duniya za ta bada damar barin gabar da ke tsakanin China da Amurka ta dauke hankalin ta, duk da illar da rikicin ke yiwa duniya.

Macron ya yi gargadin cewar janyewar Amurka daga fagen siyasar duniya zai bai wa nahiyar Turai damar samarwa kan ta tsaro da kuma rage dogaro da kayayyakin fasahar zamani da ke fitowa daga China da Amurka.

Shugaban ya ce dogaro gaba daya da wasu manyan kasashe wajen samun fasaha da abinci ko masana’antu, zai mayar da su marasa tasiri abinda zai yiwa zaman lafiyar duniya illa.

Macron ya ce annobar korona ta dada fito da muhimmancin hadin kai, sabanin yadda wasu kasashe ke bijirewa Majalisar Dinkin Duniya ko kuma dokokin ta.

Shugaban wanda ya ce za su cigaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran, ya kara da cewar za su cigaba da hadin kai da kawayen su da ke Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin sun kare ta daga rugujewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.