Wasanni

Agne Simonsson tsohon dan wasan Sweden ya rasu

Agne Simonsson tareda Tsohon dan wasan Brazil Pele
Agne Simonsson tareda Tsohon dan wasan Brazil Pele Reuters

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Sweden Agne Simonsson da ya buga wasar karshe ta cin kofin Duniya na shekara ta 1958 ya rasu ya na mai shekaru 84 a Duniya.

Talla

Jaridu a kasar ta Sweden ne suka bayar da labarin, inda suka bayar da karin haske dangane da wannan tsohon dan wasan da ya rasu ranar talata, tarihi ya nuna cewa a wasanni 51 da ya buga da kungiyar kasar Sweden ya zura kwallaye 27 kama daga shekara ta 1957 zuwa 1967.

Ya kuma haska a kasar Spain kama daga shekara ta 1960 inda ya taka leda a Real Madrid, kafin daga bisali ya cira zuwa kungiyar Real Sociedad.

An haifi Agne Simonsson ranar 19 ga watan Oktoba na shekara ta 1935.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.