Barcelona zata raba gari da Suarez

Dan wasan tsakiya na kungiyar Barcelona Luis Suarez
Dan wasan tsakiya na kungiyar Barcelona Luis Suarez REUTERS/Albert Gea/File Photo

Barcelona ta amince ta sayar da ɗan wasan tsakiyarta Luis Suarez ga Atletico Madrid kuma tana farin cikin sallamar dan wasan ko ba tare da sisin kobo ba, muddun ba wasu manyan kungiyoyin zai je ba.

Talla

Kungiyar wadda tace, tana farin cikin sallamar dan wasan ko ba tare da sisin kobo ba, muddun ba wasu manyan kungiyoyin zai je ba.

Suarez dan asalin kasar Uruguay ya amince da rage albashinsa a Atletico Madrid,bayan yunkurinsa na tafiya Juventus ya gagara saboda cikas wajen samun fasfo.

Dan haka ne ma shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya dakatar da cinikin saboda ba ya son sayar da dan wasan ga abokan hamayyarsu na Spain.

Bayan tattaunawa da wakilan Suarez, da kuma yadda yayi barazanar shaidawa manema labarai halin da ake ciki ne dai yasa Barcelona ta amince dan wasan ya tafi.

Atletico za ta biya dan wasan mai shekaru 33 kusan euro miliyan 4, bisa sharadin taimaka mata samun gurbi a Gasar Zakarun Turai, inda zai rika karbar euro miliyan 15 kowace shekara, wato rabin kudin da yake samu a Barcelona.

Luis Suarez ya kwashe sama da shekaru 6 a Barca, kuma ya zura mata kwallo har 198 a wasanni 283 da ya buga mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.