Macron ya bukaci Erdogan dangane da tattaunawa kan rikicin Meditereniya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron GONZALO FUENTES / POOL / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Turkiya Recep Tayyip Erdogan da ya shiga tattaunawar sasanta rikicin tekun Meditereniya ba tare da gindaya sharidodin da zasu dada tada hankula ba.

Talla

Yayin tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta waya, Macron ya bukaci Turkiya da ta daina yin gaban kan ta wajen daukar mataki a tekun da zai jefa shakku tsakanin ta da makotan ta.

Fadar shugaban Turkiya tace shugaba Erdogan ya bukaci Faransa ta zama mai shiga tsakani ba daukar bangare ba wajen sasanta rikicin Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.