Adadin wadanda cutar korona ta harba a nahiyar Turai ya zarce miliyan 5

Adadin wadanda cutar coronavirus ta harba a nahiyar Turai ya zarce miliyan biyar
Adadin wadanda cutar coronavirus ta harba a nahiyar Turai ya zarce miliyan biyar © Charles Platiau / Reuters

Adadin wadanda cutar coronavirus ta harba a nahiyar Turai ya zarce miliyan biyar a Larabar nan, a yayin da Faransa da Spain ke shirye shiryen tsaurara matakan takaita zirga zirga da zummar dakile yaduwar cutar a manyan biranensu.

Talla

Yanzu dai mutane kusan miliyan 32 ne suka harbu da wannan cuta a fadin duniya, yayin da sama da dubu dari 9 da 71 suka mutu tun da ta bulla a birnin Wuhan da ke tsakiyar kasar China a karshen shekarar 2019.

Bayan alamu sun nuna cewa ta shawo kan wannan cuta, ta wurin daukar matakan killacewa da rufe birane da suka yi mummunan tasiri ga tattalin arziki, yanzu Turai tana fuskantar sake bullar wannan shu’umar cuta mai saurin yaduwa, lamarin da ya sa gwamnatocin kasashen nahiyar nazartar yiwuwa daukar tsauraran matakan dakile ta.

Fiye da rabin wadanda suka harbu da wannan cuta a Turai, an same su ne a Rasha, sai kuma Faransa, Spain da Birtaniya.

Adadi na mutane dubu dari 3 da 80 da suka kamu da wannan cuta a baya bayan nan a makon da ya wuce, shine adadi mafi yawa tun da wannan annoba ta addabi duniya.

Yayin da Birtaniya ta dauki sabbin matakan taka wa wannan cuta birki, tuni shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da aniyar kasarsa ta bin sahu da wasu matakai masu tsauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.