Amurka

Amurka ta tafka hasarar dala tiriliyan 16 saboda wariyar jinsi

Hedikwatar daya daga cikin manyan bankunan Amurka Citigroup a birnin New York.
Hedikwatar daya daga cikin manyan bankunan Amurka Citigroup a birnin New York. REUTERS/Mike Segar

Daya daga cikin manyan bankunan Amurka Citigroup, ya bayyana cewar nuna wariyar jinsi a cikin shekaru 20 da suka gabata a kasar ya haifar da asarar da ta kai ta Dala triliyan 16.

Talla

Bankin ya danganta matsalar da nuna banbanci jinsi wajen biyan albashi da bada gidaje da ilimi da wasu matsalolin dake raba kan Amurka, inda yayi tayin bada Dala biliyan guda wajen tallafawa harkokin kasuwancin bakaken fata.

Shugaban bankin Michael Corbat yace shawo kan banbancin launin fata da kuma cike gibin dake tsakanin masu hali da matalauta na daga cikin manyan kalubalen da suke fuskanta wajen samar da al’umma mai kyau.

Corbat yace bankin Citigroup a shirye yake ya bude kofar taimakawa da kuma zuba jari a tsakanin bakaken fata da wasu kananan jinsina domin gina arziki da kuma samar da makoma mai kyau.

Shugaban bankin yace shawo kan wadannan banbance banbance na iya taimakawa tattalin arzikin Amurka ya sake habaka da kudin da ya kai Dala triliyan 5 a cikin shekaru 5 masu zuwa.

Matsayin bankin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da tafka mahawara kan kalaman shugaban bankin Wells Fargo wanda yace babu kwararrun bakaken fatar da zasu yiwa bankin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI