Turai

Annobar coronavirus tafi addabar kasashe 7 a Turai - EU

Wani jami'in kwana kwana, yayin aikin tsaftace gidan kula da tsofaffi masu dauke da cutar coronavirus da suka haura shekaru 60 Burbaguena, da ke kasar Spain.
Wani jami'in kwana kwana, yayin aikin tsaftace gidan kula da tsofaffi masu dauke da cutar coronavirus da suka haura shekaru 60 Burbaguena, da ke kasar Spain. © Jose Jordan / AFP

Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kungiyar tarayyar Turai EU, ta yi gargadin cewa adadin mutanen da annobar coronavirus ke kashewa na karuwa a sassan nahiyar, kuma lamarin yafi muni a kasashe guda 7, cikinsu kuwa har da Spain, da kuma Hungary.

Talla

Kasashen da hukumar dakile yaduwar cutukan kungiyar ta EU ECDC ta bayyana sun hada da Spain, Romania, Bulgaria, Croatia, Hungray, Jamhuriyar Czech da Malta.

Hukumar ta kuma zayyana wasu karin kasashen 13 cikinsu har da Faransa da Birtaniya, wadanda tace suna fuskantar karuwar yawan matasa dake kamuwa da cutar ta corona, sai dai basa fuskantar hadarin rasa rayukansu a dalilin cutar, kamar yadda lamarin yake a bangaren masu yawan shekaru.

Kwararru dai sun dora alhakin sake barkewar da annobar coronavirus ta yi a Turai kan karuwar tarukan jama’a, da kuma sauran bukukuwa a kasashen 7 da lamarin yafi muni, sai dai duk da haka hukumomin kasashen Turan sun kore yiyuwar sake rufe gidajen cin abinci da na barasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.