Di Maria ya samu haramcin wasanni 4

Angel Di Maria na PSG a wasansu da Marseille
Angel Di Maria na PSG a wasansu da Marseille Martin Bureau/AFP

Hukumar ladaftarwar gasar League 1 ta Faransa ta haramtawa dan wasan Paris Saint-Germain, Angel Di Maria buga wasanni hudu saboda samun sa da lifin tofawa wani abokin kararawarsa yawu.

Talla

Di Maria ya tofawa mai tsaron baya na Marseille Alvo Gonzalez, yawune yayin fafatawa a wani wasa mai zafi da akayı tsakanin club dinsa Paris Saint - Germain da kuma Marseille, wasan da aka tashi da jan kati har 5 a cikinsa, ciki harda Neymar, wanda yayi zargin an nuna masa wariyar launin fata.

Hukumar shirya gasar Ligue 1 din tace zata binciki zargin da Neymar ya yi na cewar Gonzalez ya nuna masa wariyar launin fata a ranar 30 ga Satumba.

Hukuncin haramtawa Di Maria wasanni 4 zai fara aiki daga ranar 29 ga watan Satumba, ma'ana da zai iya buga wasa da club dinsa zai buga da Reims a ranar Lahadi mai zuwa.

Idan zamuyiwa masu sauraro tuni dangane da abin da ya faru a wasan mai zafi na tsakiyar wannan wata, wanda ya kai ga hukumar ladaftarwar daukan wannan mataki kan Di Maria, An kori Neymar daga filin wasa saboda ya hankade Gonzalez a kafadarsa, yana mai zargin cewa dan wasan na Spain ya kira shi da “biri", zargin da Gonzalez ya musanta.

Shima dan wasan da ya fi kowa tsada a duniya Neymar kenan, ya fuskanci hukuncin haramin wasanni 2 a makon da ya gabata, saboda wannan batu dai na karawar ranar 13 ga watan Satumba a filin wasa na Parc des Princes.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.