Faransa ta sake rufe gidajen abinci da barasa saboda korona

Za'a rufe gidajen abinci da na barasa a Marseille na Faransa
Za'a rufe gidajen abinci da na barasa a Marseille na Faransa ALEJANDRO PAGNI / AFP

Faransa ta bada umurnin rufe gidaje sayar da giya da na abinci a birnin Marseille sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar korona.

Talla

Ministan lafiya Olivier Veran ya sanar da sabon matakin saboda yadda masu kamuwa da cutar suka karu a birnin.

Yanzu haka hukumomin kasar sun sanya birane 8 dake kasar cikin matakin sanya ido sosai a yunkurin da ake na shawo kan annobar, yayin da aka bukaci gidajen giya a biranen da su dinga tashi daga karfe 10 na dare.

Yayin da abangare daya, ‘Yan Majalisun Dokokin Faransa sun amince da matakin bai wa dandazon jama’a damar shiga filayen wasanni a yankunan da cutar coronavirus ke da karancin yaduwa.

A halin yanzu kimanin mutane dubu 5 aka amincewa shiga filayen wasanni a lokaci guda a Faransa, amma adadin bai wuce dubu 1 ba a yankunan da cutar ta fi kamari, kamar birnin Marseille.

Wannan doka ta takaita ‘yan kallo a filayen wasanni, ita ce ta tilasta wa kungiyar kwallon kafa ta Marseille buga wasanta da Lille a makon jiya tare da ‘yan kallo kimanin dubu 1 duk da cewa filinta na daukar nauyin mutane dubu 67.

A yanzu dai ‘yan majalisar dokokin na Faransa kamar Sacha Houlie na jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron na ganin cewa, ya dace a sauya wannan doka domin bai wa dandazon ‘yan kallo damar shiga filin wasa koda kuwa mutane ba za su mutunta sharuddan kare kai daga kamuwa da cutar corona ba.

Tuni dai ‘yan majalisun suka kada kuri’ar amincewa da matakin yi wa dokar kwaskwarima, suna masu jaddada muhimmancin ‘yan kallo ga tattalin arzikin kungiyoyin kwallon kafa na Faransa.

Kodayake dole ne a gabatar da kudirin na ‘yan majalisun ga Majalisar Tarayya nan da ranar 1 ga watan Oktoba domin ta bayyana matsayarta a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.