Faransa

Karin mutane dubu 16 sun kamu da cutar coronavirus a Faransa

Mutane sanye da takunkuman rufe baki da hanci a kusa da hasumayar Eiffe da ke birnin Paris a Faransa.
Mutane sanye da takunkuman rufe baki da hanci a kusa da hasumayar Eiffe da ke birnin Paris a Faransa. Charles Platiau / Reuters

Hukumomin Faransa sun ce mutane dubu 16 da 96 suka kamu da cutar coronavirus jiya alhamis, a daidai lokacin da al’ummar kasar ke korafi kan matakan da gwamnati ta dauka na taikaita lokacin bude gidajen sayar da giya da kuma abinci.

Talla

Gwamnatin Emmanuel Macron ta sanar da daukar sabbin matakan ne domin dakile yaduwar cutar, matakin da ya gamu da suka daga Magadan Garin Paris da Marseille da kuma wasu jama’a.

Daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka har da na hana taruwar jama’ar da suka wuce 10 a lokaci guda, da kuma hana zuwa kallon kwallo ko bikin rawa na mutanen da suka wuce 1,000.

Yanzu haka dai jami’an biranen Paris da Marseille sun bayyana matukar bacin ransu kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na takaita lokutan harkokin jama’a domin dakile yaduwar cutar tacoronavirus.

Mataimakin Magajin Garin birnin Marseille, Benoit Payan yace an dauki matakin hukunta birnin na su ne kawai ba tare da hujja ba, yayin da mai rike da mukamin Magajin Garin Paris, Anne Hidalgo tace ta gabatar da korafi akai, domin babu dalilin da za’a rufe gidajen barasa da karfe 10 na dare.

Ministan lafiya Olivier Veron ya sanar da matakin wanda ake saran ya fara aiki daga ranar asabar mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.