Faransa

Faransa na bincike kan farmakin da aka sake kaiwa jaridar Charlie Hebdo

Harabar tsohon ofishin jaridar Charlie Hebdo da aka sake kaiwa farmaki a birnin Paris.
Harabar tsohon ofishin jaridar Charlie Hebdo da aka sake kaiwa farmaki a birnin Paris. AP Photo/Thibault Camus

Hukumomin tsaron Faransa sun kaddamar da bincike kan farmakin da aka sake kaiwa ofishin jaridar zanen barkwanci ta Charlie Hebdo a jiya Juma’a, inda akalla mutane 4 suka jikkata.

Talla

Tuni dai yan Sanda suka kama mutumin da ake tuhuma da kai farmakin na wuka, da kuma karin wasu mutane 6 da ake kyautata zaton sun taimaka wajen kai harin.

Masu gabatar da kara kan laifukan ta’addanci a Faransa sun ce akwai alaka tsakanin maharan da kungiyoyin 'yan ta'adda, wadanda suke kyautata zaton su ne suka kitsa kaiwa tsohon ginin mujallar ta Charlie Hebdo harin, sakamakon cin zarafin al’ummar Musulmi da ta yi, ta hanyar sake wallafa zanen hoton Annabi Muhammad salallahu alaihi wa sallam.

A farkon watan Satumban da muke, shugaban Faransa Emmnauel Macron ya yi kakkausar suka kan mutanen da ke neman shaidar zama a kasar amma su ke bijirewa wasu daga cikin dokokinta ciki har da ‘yancin cin zarafi ko batanci da kundin tsarin mulki ya sahale, batun da shugaban ke cewa kowa na da cikakken ‘yancin dariya da caccaka da ma cin zarafi ko tsokana bisa tanadin doka.

Emmanuel Macron ya bayyana haka ne yayin jawabinsa na bikin cika shekaru 150 da zaman Faransa kasa Jamhuriyya, inda ya ce ga duk mai son zama bafaranshe tofa dole ne ya karbi dukkannin tanadi da dokokin kasar sabanin zabar wani sashe tare da yin watsi da wani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.