Belarus

'Yan sandan Belarus sun kame masu zanga-zanga dubu 12 cikin watanni 2

Zanga-zangar adawa da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko
Zanga-zangar adawa da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko REUTERS/Vasily Fedosenko

Jami’an tsaron Belarus sun sake kame masu zanga-zanga akalla 80 cikin karshen makon nan a babban birnin Minsk, yayinda dubban yan kasar ke cigaba da neman tilastawa shugaba Alexender Lukashenko yin murabus, yunkurin da suka soma a farkon Agustan da ya gabata.

Talla

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce ‘yan sanda sun kama masu zanga-zangar ne bayan kure musu gudu a sassan birnin na Minsk.

Kungiyoyin fararen hular sun ce kawo yanzu jumillar masu zanga-zanga dubu 12 jami’an tsaron kasar ta Belarus suka kame, tun bayan soma boren adawa da wa’adin mulkin shugaba Alxender Lukashenko karo na 6.

Ikirarin lashe zaben ranar 9 ga watan Agusta da Lukashenko yayi ne ya haddasa zanga-zangar mafi girma da kuma dadewa a tarihin kasar ta Belarus, tun bayan samun ‘yancin kai daga Tarayyar Soviet a shekarar 1991.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.