Armenia-Azerbaijan

Kusan mutum 30 sun mutu a rikicin kan iyakar Armenia da Azerbaijan

Iyakar Armenia da Azerbaijan da ake ci gaba da tafka rikici a kansa.
Iyakar Armenia da Azerbaijan da ake ci gaba da tafka rikici a kansa. Defence Ministry of Azerbaijan/Handout via REUTERS

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a rikici tsakanin Armenia da Azerbaijan ya tasamma 30 dai dai lokacin da aka shiga rana ta biyu ana gwabza fada tsakanin kasashen biyu da ke da tarihin yaki tun shekaru 30 da suka gabata.

Talla

Tun da safiyar yau Litinin ne shugaba Ilham Aliyev na Azerbaijan ya yi umarnin girke jami’an tsaro a yankin na Nagorny Karabakh da kasashen biyu ke rikici a kansa, inda ya bukaci gaggauta kawo karshen zubar da jinin wanda ya faro tun jiya Lahadi.

Yankin na Nagorny Karabakh da ya balle daga Azerbaijan tare da ayyana kansa a matsayin kasa mai cin gashin kanta tun a 1990 bayan yakin basasar da ya kai ga kisan mutane akalla dubu 30, ko da yak e kawo yanzu kasashen Duniya na kallonshi a yankin Azerbaijan duk da yunkurin Armenia na kokarin mamaye shi.

Sabon rikicin na Azerbaijan da Armenia da ya birbishinsa ya faro a shekarar 2016, gabanin tsanantarsa watanni 4 da suka gabata wanda yak ai ga kisan dakarun kasashen biyu, ya sanya fargabar yiwuwar fuskantar makamancin yakin na shekaru 30 da suka gabata, ko da ya ke tuni Turkiya da ke matsayin kawa ga Azerbaijan ta gargadi Armenia kan ci gaba da mamayar yankin na Karabakh yayinda a bangare guda Tarayyar Turai ta kakkausar suka ga yunkurin kasashen duniya na katsalandan a rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.