Mutane da cutar korona ta kashe sun zarce miliyan guda

Ma'ikatar kiwon lafiya dake kula korona a Faransa
Ma'ikatar kiwon lafiya dake kula korona a Faransa Christophe SIMON / AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya tace adadin mutanen da cutar korona ta kashe a duniya ya zarce miliyan guda, tun bayan barkewar ta a China, a watan Disambar bara.

Talla

Tuni wannan annoba ta lalata tattalin arzikin kasashen duniya da dama da haifar da matsaloli da dama a kasashen duniya musamman ga ma’aikata da marasa galihu.

Kasar Amurka ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka mutu, inda take da sama da 200,000, sai kasashen Brazil da India da Mexico da kuma Birtaniya.

Yanzu haka cutar da ta haifar da matsaloli da dama, a nahiyar Turai ta sake dawowa, abinda ya sa shugabannin yankin ke daukar sabbin matakai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.