Jagorar 'yan adawan Belarus za ta yi jawabi a majalisar dokokin Faransa

Jagorar 'yan adawan Belarus, Svetlana Tikhanovskaïa.
Jagorar 'yan adawan Belarus, Svetlana Tikhanovskaïa. Sergei GAPON / AFP

Jagorar ‘yan adawan Belarus ta ce za ta gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin Faransa, bayan tataunawarta da shugaba Emmanuel Macron, wanda ya yi alkawarin taimakawa ta wajen shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.

Talla

Svetlana Tikhanovskaya ta shaida wa kamfanin dillancin Labaran Faransa AFP cewa ta samu gayyata don gabatar da jawabi a majalisar, kuma ta amsa.

Ganawar da ta yi da Macron ita ce mafi girma da mahimmanci ya zuwa yanzu tun bayan zaben kasar mai cike da cece kuce a watan da ya gabata, zaben da ta yi ikirarin samun galaba a kan shugaban kasar mai ci Alexander Lukashenko.

Tikhanovskaya ta taba gabatar da jawabi a gaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, da kuma majalisar dokokin Turai, kuma ta gana da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar Tarayyar Turai, sannan ta gana da shugabannin kasashen Poland da Lithuania.

Shugaba Emmanuel Macron ya shaida wa manema labarai bayan ganawarsa da jagorar ‘yan adawan cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo karshen rikici a kasar, ta wajen shiga tsakani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.