MDD za ta yi taron gaggawa a game da rikicin Armenia da Azerbaijan

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. ©REUTERS/Carlo Allegri

Yau ake saran kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa kan yakin da ya barke tsakanin Armenia da Azerbaijan dangane da mallakar Yankin Nagorny Karabakh da kasashen biyu ke rikici akai.

Talla

Majiyoyin diflomasiya sun ce kasar Belgium ce ta bukaci gudanar da taron, wanda ya samu goyan bayan kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya, kuma za’a gudanar da shi ne a asirce da misalin karfe 5 na yamma agogon New York.

Wannan musayar wuta tsakanin kasashen Armenia da Azerbaijan na zuwa ne a daidai lokacon da ake gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

Ya zuwa yanzu an kwashe kwanaki biyu ana fafatwa tsakanin dakarun kasashen biyu, yayin da ma’aikatar tsaron Karabakh ta ce tayi asarar sojoji 84 bayan fararen hula 11.

Shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev ya bukaci kara yawan sojoji a bakin daga, yayin da shugaban soji Janar Mais Barkhudarov ya sha alwashin sadaukar da ran shi domin kare martabar kasar.

Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Armenia Artsrun Hovhannisyan ya zargi dakarun Azerbaijan da kai munanan hari akan iyakar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI