Azerbaijan-Armenia

Faransa ta yi gargadin yiwuwar rincabewar rikicin Azerbaijan da Armenia

Faransa ta yi gargadin yiwuwar rikici tsakanin Azerbaijan da Armenia kan yankin Nagorny Karabakh ya bayar da damar shigowar mayakan ketare don bai wa hammata iska, la’akari da yadda alamu ke nuna bangarorin biyu basu da shirin jaa da baya a fadan wanda zuwa yanzu ya lakume rayuka fiye da 100 cikin kasa da mako guda da farawa.

Rikici tsakanin kasashen biyu makotan juna da aka shafe tsawon shekaru ana yi, a lahadin da ta gabata ne ya dawo sabo fil.
Rikici tsakanin kasashen biyu makotan juna da aka shafe tsawon shekaru ana yi, a lahadin da ta gabata ne ya dawo sabo fil. Defence Ministry of Azerbaijan/Handout via REUTERS
Talla

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian a wata zantawarsa da shugabannin kasashen Armenia da Azerbaijan ta wayar tarho a safiyar yau Juma'a, ya gargadesu kan yadda rikicin ke kokarin shiga wani yanayi da za a gaza warware shi cikin lumana.

Ofishin harkokin wajen Faransar ya sanar da cewa yayin zantawar ta Le Drian da shugabannin na Azerbaijan da Armenia ya bayyana musu hadarin da ke tattare da shigowar mayaka daga ketare a wani yunkuri na ingiza rikicin.

Faransa wadda karara ke goyon bayan Armenia kan mamayar da ta ke yiwa yankin na Nagorny Karabakh da ya balle daga Azerbaijan ko a jiya Alhamis shugaban kasar Emmanuel Macron ya nemi karin bayani daga takwaransa na Turkiya Recep Tayyib Erdogan kan zargin da ke cewa tarin mayakan Syria da Libya sun ratsa ta kasarsa zuwa Azerbaijan don taimakawa a fadan.

Macron wanda su ke ci gaba da takun saka da Erdogan na Turkiya kan batutuwa da dama, yayin jawabinsa a taron EU can a Brussels ya ce, bayanan sirrin da aka tattara, sun nuna cewa, kimanin mayaka 300 aka kwaso daga birnin Aleppo na Syria, inda suka ratsa ta birnin Gaziantep na Turkiya domin isa Azerbaijan.

Kasashen biyu wadanda ke da tsohuwar gaba kuma suka taba gwabza yaki a shekarun 1990 da 2006 a Lahadin da ta gabata ne rikicin ya dawo sabo bayan tsanantar tankiya tsakaninsu a farkon shekarar nan kan yankin na Karabakh da Armenia ke ci gaba da mamayewa duk da kasancewarsa wani yanki na Azerbaijan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI