Tabargazar masu tsatsauran ra'ayi na illa ga Musulunci - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Ludovic Marin/Pool

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya kaddamar da wani shirin kare martabar kasar a matsayinta ta wacce babu ruwanta da addini daga tsatsauran ra’ayin Islama.

Talla

A wani jawabin da aka dade ana dako, Macron ya ce babu daga kafa a sabon yunkurin da ake na rabe addini da harkokin ilimi da na gwamnati a Faransa.

Ya ce ba a Faransa kadai ba, a duk fadin duniya addinin Islama ya shiga wani mawuyacin hali sakamakon tabargazar masu tsatsauran ra’ayi.

Ya bada sanarwar cewa gwamnatinsa za ta gabatar da wani kudiri a watan Disamba dazai karfafa dokar nan ta 1905, wacce ta rabe tsakanin majami’a da gwamnati.

ya ce dokar ta baiwa al’umma damar yin addinin da suke so, amma kuma ba za ta lamunci gudanar da ayyukan da suka shafi addini a makarantu da ma’aikatun gwamnati ba.

Wadannan matakai in ji Macron, ana daukar su ne da zummar warware matsalolin ta’addancin da sunan addinin Islama a Faransa, tare da inganta zamantakewa.

Ya sanar da cewa Faransa za ta lalubo hanyar ceto Musulunci a kasar daga mummunan tasirin kasashen waje, ta hanyar inganta sa ido a kudaden da ke shigowa masalatai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.