Jamus

Jamusawa sun yi zanga-zangar kin zaman gida

Dubban masu zanga-zanga sun gudanar da tattakin nuna adawa da matakin kulle jama’a a gidajensu a kudancin kasar Jamus kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka bayyana.

Masu zanga-zangar na adawa da matakin kulle jama'a a gidajensu don hana bazuwar cutar coronavirus.
Masu zanga-zangar na adawa da matakin kulle jama'a a gidajensu don hana bazuwar cutar coronavirus. REUTERS/Christian Mang
Talla

Kodayake jagororin zanga-zangar sun gaza cimma manufarsu ta jerin gwanon jama’ar da yawanta ya kai dubu 200 a kusa da tafkin Constance, yayin da a banagre guda aka samu wasu mutane daban da suka fito domin nuna goyon bayansu ga matakin da gwamnati ta dauka na kulle jama’a don hana bazuwar cutar coronavirus.

Kimanin mutane dubu 10 zuwa dubu 11 daga bangarorin biyu suka fantsama kan tituna domin gudanar da boren a cewar majiyar ‘yan sanda.

Hukumomin Lafiya sun jinjina wa gwamnatin Jamus kan yadda ta samu nasarar takaita yaduwar annobar Covid-19 tsakanin al’ummarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI