Faransa

Faransa za ta sake kulle Paris saboda korona

Za a takaita zirga-zirga a birnin Paris saboda sake barkewar coronavirus.
Za a takaita zirga-zirga a birnin Paris saboda sake barkewar coronavirus. Charles Platiau / Reuters

Gwamnatin Faransa na shirin sanya sabbin matakan takaita walwalar jama’a don dakile yaduwar cutar Covid-19, kuma daga wannan Litinin za a rage yawan zirga-zirga musamman a babban birnin Paris.

Talla

Faransa wadda a baya-bayan nan ke fuskantar karuwar sabbin masu kamuwa da cutar ta Covid-19 ta sanar da haramcin shigaowar baki tsakar birnin Paris yayin da aka yi umarnin kulle ilahirin wuraren taruwar jama’a ciki har da wuraren shakatawa da shagunan barasa.

A cewar Ministan Lafiyar kasar Olivier Veran, ta hanyar daukar matakin ne kadai za a dakile yaduwar cutar ta Covid-19 bayan da a Asabar din da ta gabata kadai Faransa ta samu adadin mutum dubu 16 da 972 sabbin kamuwa da coronavirus, adadin  da ke matsayin mafi yawa da kasar ta gani tun bayan barkewar cutar.

Hukumuar kididdiga ta Faransar ta nuna cewa mutum 250 cikin duk mutum dubu guda na cikin hadarin kamuwa da cutar ta Covid-19 a tsakar birnin Paris, alkaluman da ma’aikatar lafiyar ke cewa ya zama wajibi gindaya kwarya-kwaryan matakan killace jama’ar.

Tuni dai cutar ta tsananta a kudancin kasar ta Faransa ciki har da Marseille da kuma Guadeloupe.

Daraktan hukumar kididdigar Aurelien Rousseau cikin sakon da ya wallafa a Twitter ya ce matakin killace jama’ar ne kadai za abi don dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.