Wasu kwararru 3 sun lashe kyautar Nobel, saboda gano cutar hanta

Mutane 3 da suka lashe kyautar Novel, Harvey Alter, Michael Houghton,da aka karrama 05 ga watan Oktoban 2020
Mutane 3 da suka lashe kyautar Novel, Harvey Alter, Michael Houghton,da aka karrama 05 ga watan Oktoban 2020 Nobel Prize

Kwararru uku kan kiwon lafiya da suka hada da Harvey Alter, da Charles Rice dukkaninsu Amurkawa da kuma Michael Houghton dan Birtaniya, sun lashe kyautar ‘Nobel’ lambar yabo ta girmamawa a fannin lafiyar da suka yi fice.

Talla

Kwamitin da ke tantance wadanda suka cancanci kyautar lambar yabon ta Nobel a fannoni daban daban, ya ce an karrama kwararrun na Amurka da Birtaniya ne bisa gagarumar gudunmawar da suka bayar ta gano kwayar cutar 'Hephatitis C' da ke haifar da nau’ikan cutukan hanta ciki har da sankararta, abin da ya share hanyar samar da magungunan cutar, wadda ke yaduwa ta hanyar jini da kuma jima’i.

A baya bayan nan hukumar lafiya ta duniya WHO ta kiyasta cewar, akwai akalla mutane miliyan 70 da suke dauke da kwayar cutar ta 'Hephatitis C' a sassan duniya, cutar da ke halaka kimanin mutane dubu 400 duk shekara.

Kwararru dai sun tabbatar da cewa, alamomin kwayar cutar hantar ta 'Hephatitis C' sun hada da rashin son cin abinci, haraswa, kasala da kuma shawara.

A shekarar 1976 aka gano kwayar cutar hanta ta Hephatitis B, sai dai hakan bai magance kirshirwar masana ta neman karin bayanai kan cutar ba, har zuwa wannan lokaci da bayanan kwararrun suka tabbatar da cewa gano kwayar cutar hantar ta 'Hephatitis C' ya ceto rayukan miliyoyin mutane daga halaka.

Kwamitin bada kyautukan lambar yabon ta Nobel ya ce an karrama Harvey Alter ne bisa gudunmawarsa ta nazartar yanayin masu ciwon hanta da aka yi wa karin jini, inda ta hakan ya gano cewar da da dama sun kamu da kwayar cutar Hephatitis C ne, a maimakon 'Hephatitis A' ko B da ake zato.

Shi kuwa Michael Houghton ya samu tashi kyautar ce bisa kokarinsa na gano yadda sabuwar kwayar cutar hantar ta 'Hephatitis C' ke ginuwa, yayin da shi kuma Charles Rice mai shekaru 68, ya gano hujjojin da ke tabbatar da cewa kwayar cutar 'Hephatitis C' ce kadai ke haddasawa wadanda suka kamu da ciwon hanta rashin lafiya.

Dukkanin kwararrun 3, za su raba kyautar akalla dala miliyan 1 da 100, a matsayin ladan gagarumar gudunmawarsu ga fannin kiwon lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI