Faransa

Kuraye 7 sun tsere daga gandun dajin Faransa

Hukumomin Faransa sun yi gargadi ga mazauna kudancin kasar dangane da bacewar wasu kuraye guda 7 wadanda suka tsere daga inda ake tsare da su, bayan ambaliyar ruwa ta shafi gidajen da ake tsare da su a karshen mako.

Wasu kuraye a Gandun Dajin Faransa.
Wasu kuraye a Gandun Dajin Faransa. AFP
Talla

Yanzu haka hukumomin suna can suna farautar wadannan kuraye wadanda suka gudu daga gandun dajin birnin Nice, sakamakon ambaliyar da ta hallaka mutane 4.

Daraktan hukumar da ke kula da gandun dajin Eric Hansen ya ce kurayen ba za su iya cigaba da rayuwa da kan suba, saboda yadda aka saba basu abinci, wanda ke nuna yiwuwar yunwa ta iya yi musu illa.

Sai dai Mr Eric Hansen ya ce anzu haka sun mayar da hankali wajen ganin an gano kurayen domin kama su kafin su yi ta’addi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI