Mata biyu sun lashe kyautar Nobel ta kimiyyar sinadarai

Ba Faranshiya Emmanuelle Charpentier da Ba-Amurkiya Jennifer Doudna, da suka lashe kayautar Nobel ta Chemistry
Ba Faranshiya Emmanuelle Charpentier da Ba-Amurkiya Jennifer Doudna, da suka lashe kayautar Nobel ta Chemistry Nobel Prize

A karon farko tawagar mata zalla ta lashe kyautar lambar yabo ta Nobel a bangaren kimiyyar sarrafa sinadarai wato Chemistry, wadanda aka karrama su a Larabar nan. 

Talla

Eammanuelle Charpentier Ba-Faranshiya mai shekaru 52, da kuma Jennifer Doudna ‘yar Amurka mai shekaru 56, sun kafa tarihin baiwa fannin kimiyyar Sinadarai gudunmawa ne ta hanyar kirkirar fasahar ta sarrafa kwayoyin halittar dan adam, dabba, kananan halittu, da kuma tsirrai cikin sauki, sauri da kuma taka tsan-tsan, wadda a kimiyyance ake kira da CRISPR-Cas9.

Kwamitin kwararrun da ke bada lambar yabon ta Nobel ya bayyana sabuwar fasahar sarrafa kwayoyin halittun ta CRISPR-Cas9 da matan suka kirkiro, a matsayin juyin juya hali a fannin kimiyyar hallitu masu rai, matakin da zai bada damar bunkasa dabarun warkar da cutar kansa.

Zalika akwai kwarin giwar cewa nan gaba kadan fasahar sarrafa kwayoyin hallitun za ta bada damar magance wasu cutukan da ake gada daga iyaye da kakanni.

Baya ga lambar yabo ta Nobel, Charpentier da Doudna sun kuma lashe kyautar dala miliyan 1 da 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.