Faransa ta zargi Turkiya da tura soji yankin Karabakh da ake rikici

Yadda akayi ta harba makamai yankin Karabakh
Yadda akayi ta harba makamai yankin Karabakh Bars Media Documentary Film Studio via REUTERS

Faransa ta soki kasar Turkiya da amfani da sojoji don marawa Azerbaijin baya, a yakin da take yi da Armenia dangane da takaddamarsu kan yankin Nagorno-Karabakh.

Talla

A cewar Ministan waje na Faransa Jean Yves Le Drain, dabarar itace akwai sojan Turkiya a ciki, al’amarida ke kara dama lissafi da fadada wannan yaki sosai.

Kasashen biyu, Armenia da Azerbaijin dake cikin tsohuwar Soviet na zaman doya da manja na tsawon shekaru gameda halaccin yankin Nagorno-Karabakh, wanda kabilun Armenia ke ciki bayan ficewa daga Azerbeijin da yakin wancan lokaci da yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu 30.

Ranar 27 ga watan jiya ne dai yaki ya sake barkewa tsakanin kasashen biyu.

Komawa wannan yaki da ya janyo kasashen yankin shiga ciki inda Turkiya ke goyon bayan Azerbaijin yayinda Armenia ke fatan kawayenta kamar Rasha ta shiga ciki ta mara mat abaya.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya fadi cewa Turkiya ta gayyaci masu jihadi daga Syria zuwa yankin.

Ministan waje na Faransa na cewa akwai taro a Geneva yau, sannan kuma littini mai zuwa a Moscow don duba wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.