Faransa

Google zai fara biyan kafofin labaran Faransa Ladan labaransu da ke shafinsa

Kotun ta Faransa ta ce wajibi ne Google ya biya kamfanonin labaran 3 ladan euro dubu 20 kowannensu.
Kotun ta Faransa ta ce wajibi ne Google ya biya kamfanonin labaran 3 ladan euro dubu 20 kowannensu. Reuters

Kotun daukaka kara a birnin Paris na Faransa ta umarci kamfanin Google na Amurka ya tattauna da wasu kafofin yada labaran kasar don fara biyansu ladan labaransu da ake karantawa ta shafin.

Talla

A hukuncin wanda aka dade ana jira, kan takaddamar dake tsakanin kamfanin na Google da wasu kungiyoyin kafafen yada labarai na Faransa, da ke neman wani kaso cikin kudin shigar da kamfanin na Amurka ke samu, da suka kira da hakkin makwabtaka.

Kotun ta bukaci kamfanin na Google ya tattauna da wadannan kungiyoyin uku don fasalta kason da ya kamata ya rika biyansu kan labaran da su ke wallafa da kai tsaye mutane kan iya karantawa ta shafin na google.

Kotun wanda ta yi watsi da bukatar Google da ke neman neman kaucewa biyan kungiyoyin ladan labaran, ta bayyana cewa wajibi ne Google ya biya kafofin labaran 3 euro dubu 20 kowannensu.

Wakilan Kungiyoyin uku da zasu fara karbar wadanan kudade kafin shiga tattaunawar ci gaba da biyan hakkokin nasu, sun hada da hadakar kungiyar kafofin yada labarai, da kungiyar mujallu da jaridu da kuma kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Wannan mataki dai zai taimakawa kafofin yada labaran Faransan farfadowa daga koma bayan tattalin arziki da suka samu kansu saboda annobar korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI