Faransa

Faransa ta tsaurara matakai a biranen ta saboda korona

Wani bangare na birnin Paris
Wani bangare na birnin Paris REUTERS/Charles Platiau/File Photo

Gwamnatin Faransa ta sanya biranen kasar guda 4 karkashin kulawar kololuwa sakamakon karuwar masu harbuwa da cutar korona, abin da ya kara yawan adadin biranen da matakin ya shafa a sassan kasar.

Talla

Ministan Lafiya Olivier Veran ya bayyana biranen da sabon matakin ya shafa da suka hada da Birnin Lille da Lyon da Grenoble da kuma Saint-Etienne.

Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa Aurelien Rousseau ya ce ya zama wajibi su dauki kwararan matakai domin dakile sake dawowar cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ya zuwa yanzu mutane miliyan 36 da dubu 200 suka kamu da cutar a duniya, kuma miliyan guda da dubu 57,084 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.