Majalisar EU na son matsin lamba kan rage turiri a Turai
Wallafawa ranar:
Majalisar Tarayyar Turai ta bukaci kungiyar ta matsa lamba ga kasashe mambobinta wajen ganin sun rage yawan turiri mai gurbata muhallin da suke fitarwa a kokarin shawo kan matsalar dumamar yanayin a duniya.
Tun farko wakilan kasashe mambobin EU da ke cikin Majalisar ne suka kada kuri’ar da ke neman rage yawan turirin hayaki mai gurbata muhallin da ke fita tsakanin kasashen kungiyar da akalla kashi 60 nan da shekarar 2030, kaso mafi yawa da kungiyar ke neman zabtarewa fiye da yadda tun farko ta bayyana .
Kazalika mambobin Majalisar ta EU sun kuma bukaci tabbatar da ganin kungiyar ta jajirce wajen cimma muradun yaki da dumamar yanayi kafin shekarar 2050.
Kuri’ar mambobin na Majalisar Turai, wani bangare ne na tattaunawar da kasashen ke fatan yi nan gaba kadan don cimma jituwa kan hakikanin adadin hayakin da za su zaftare a kasashen nasu don tunkarar matsalar ta dumamar yanayi wadda duniya ke fuskanta.
Kasashen Faransa da Jamus dai na matsayin ‘yan gaba-gaba da ke neman ganin an cimma jituwar game da matsalar ta dumamar yanayi, kodayake suna fuskantar suka daga kasashen gabashin nahiyar wadanda tattalin arzikinsu ya dogara kan albarkatun Coal, sinadari mafi haddasa dumamar yanayi sakamakon yadda ake aikin hako shi.
Bayan nasarar Jam’iyya mai yaki da dumamar yanayi wajen jagorantar Majalisar ta Turai ne, gangamin yaki da dumamar yanayin a nahiyar ya samu karfi inda Majalisar ke shirin jagorantar taro kan batun ko dai a mako mai zuwa ko kuma cikin watan Disamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu