Messi ya kama hanyar cikan burinsa na neman kofin duniya

Kaftin din Barcelona Lionel Messi.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi. REUTERS/Albert Gea

Gwarzon dan wasan duniya Lionel Messi ya sanya matsalolinsa na Barcelona, ya samowa kasarsa Argentina tikitin shiga gasar neman cin kofin Duniya, bayan doke kasar Ecuador da ci 1 - 0 a wasan da suka kara Jumma'an nan. 

Talla

Dan wasan mai shekaru 33 ya kasance cikin rikici da kungiyarsa ta Barcelona, amma hakan bai karya masa guiwa ba, a karsashin da ya nuna a wasan, inda ya ci kwallo ta bugun fanaretin mintuna 13 da soma wasa.

Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau 6, yayi ta kokarin barin Barcelona a karshen kakar badi, amma ya fuskanci cikas, to amma alamu ya nuna ya fi farin ciki a cikin rigar kwallo mai ruwan shudi da fari ta kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.