Wulakancin Barcelona ya sani zubda hawaye - Suarez

Dan wasan gaba na Atletico Madrid Luis Suarez
Dan wasan gaba na Atletico Madrid Luis Suarez Josep LAGO / AFP

Tsohon dan wasan Barcelona Luis Suarez da yanzu haka yake taka leda a Atletico Madrid, yace Wulaƙancin da Barcelona ta yi masa har ya sa shi kuka kafin ya koma Atletico.

Talla

Dan wasan dan asalin kasar Uruguay ya bar Barcelona a watan Satumba bayan ya kwashe shekara 6 yana murza tamola, yana mai cewa sai da aka dakatar da shi yin atisaye da sauran 'yan wasan kungiyar kafin ya rabu da su, to amma yanzu ya samu kansa cikin natsuwa.

A shekarar 2014 Suarez ya je Barcelona daga Liverpool a kan £74m, kuma ya kasance dan wasa na uku da ya fi ci mata kwallo, bayan zura kwallaye har 198.

Suarez, ya taimakawa Barcelona lashe Kofin La Liga hudu, Kofin Copa del Reys hudu, Kofin Zakarun Turai daya da kuma Kofin Gasar Lig ta Duniya guda daya a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.