Armenia da Azerbaijan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Daya daga cikin sassan Stepanakert, babban birnin yankin Nagorno-Karabakh da kasashen Armenia da Azerbaijan ke gwabza yaki akai.
Daya daga cikin sassan Stepanakert, babban birnin yankin Nagorno-Karabakh da kasashen Armenia da Azerbaijan ke gwabza yaki akai. ARIS MESSINIS / AFP

Ministan harkokin wajen Rasha Sregie Lavrov ya ce kasashen Armenia da Azerbeijan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yakin da suka shafe kimanin mako 2 suna gwabzawa kan mallakar yankin Nagorno-Karabakh.

Talla

Yarjejeniyar kuma za ta soma aiki ne daga karfe 12 ranar yau asabar, tare da alkawarin soma wata tattaunawar don cimma yarjejeniyar sulhu ta dindindin.

Yakin na Azerbeijan da Armenia yayi sanadin mutuwar fararen kusan 60, da sojoji akalla 370 daga dukkanin bangarorin, yayinda wasu 168 suka jikkata, daga ranar 27 ga Satumban da ya gabata zuwa wanna lokaci.

Rikicin kasashen dai shi ne mafi muni da aka gani tun bayan yakin da suka gwabza tsakaninsu tsakanin shekarar 1991 zuwa 1994, inda kimanin mutane dubu 30 suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.