Faransa

COVID-19: Dokokin takaita walwalar jama'a sun soma aiki a biranen Faransa

Wai bangaren birnin Paris yayin da jama'a ke zirga zirga.
Wai bangaren birnin Paris yayin da jama'a ke zirga zirga. Gonzalo Fuentes/Reuters

Yau asabar dokoki masu tsauri na takaita walwalar jama’a za su soma aiki a wasu daga cikin manyan biranen Faransa, da suka hada da Lille, Lyon, Grenoble, da Saint-Etienne, domin dakile annobar coronavirus da ta sake bakewar a kasar karo na biyu.

Talla

Jiya Juma’a, ma’aikatar lafiyar Faransa ta ce a karon farko tun bayan bullar annobar coronavirus cikin kasar, an samu adadin mutane sama da dubu 20 da suka kamu da cutar a rana guda.

Alkalumman da ma’aikatar lafiyar ta fitar a daren jiya Juma’a, sun nuna cewar mutane dubu 20 da 330 ne aka gano sun kamu da cutar cikin sa’o’i 24, abinda ya sanya jumillar adadin wadanda annobar ta harba a kasar kaiwa dubu 691 da 977.

Dangane da wadanda annobar ke halakawa kuwa, a yanzu adadin rayukan da suka salwanta a Faransar ya kai dubu 32 da 630, bayan samun Karin mutane 109 da cutar da kashe a kasar.

Kawo yanzu kuma, jumillar mutane dubu 7 da 864 annobar ta tilasta kwantarwa a asibitocin dake daukacin kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI